Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (AS) – ABNA - ya habarta cewa: Jaridar Isra'ila "Maariv" a cikin wani rahoto game da abubuwan da suka faru a shekara da ta wuce, ta yi nuni da cewa tsayin dakar Iraniyawa da Hizbullah ta Lebanon ya tabbatar wa Isra'ila cewa tana fuskantar abokan gaba da ba a zata ba.
A daidai lokacin da ake fitar da wannan rahoto, "Robert O'Brien" tsohon mai ba da shawara kan tsaron ƙasar Amurka shi ma a cikin hira da jaridar Maariv ya ce: Ina ganin muna gab da cimma yarjejeniya da Iran. Da aka tambaye shi ko sakamakon tattaunawar zai iya kai wa ga yarjejeniya irin ta JCPOA? Ya ce: A'a, ina ganin yarjejeniya za ta fi kyau. Ina fata yarjejeniyar da za a kulla za ta iya haifar da daidaita dangantaka da bunƙasar tattalin arziki a yankin kuma ta kawo ƙarshen yaƙi.
Jaridar Maariv a ci gaba da rahotonta na nazari ta bayyana cewa: durkufar da Iraniyawa da Hizbullah abu ne mai wuya da wahala; domin suna da ƙarfin juriya sosai.
Wannan kafar yaɗa labarai ta Isra'ila ta jaddada cewa: Wannan yanayin na iya jefa Isra'ila zuwa yaƙin maras ƙarewa.
Ikrarin Cewa Ba Za A Iya Cin Galaba Kan Iran Ba
Tun da farko ma, jaridar Maariv a cikin wani rahoto game da rashin yiwuwar cin nasara kan Iran ga makiya ta rubuta cewa: Trump da Netanyahu sun gane cewa ba zai yiwu a ci nasara kan Iran ba, kuma dole ne su amince da cewa wannan ƙasa za ta ci gaba da kasancewa babbar ƙasa mai ƙarfin nukiliya.
Wannan jaridar ta kara da cewa: Trump da Netanyahu sun kuma gane cewa Hizbullah za ta ci gaba da wanzuwa, kuma Washington na neman hanyoyin tuntuba da ita. Wannan yana faruwa ne a daidai lokacin da Netanyahu a yanzu kafin zaɓen Knesset (majalisar dokokin gwamnatin yahudawa) ke neman nasara a kan zirin Gaza da mazaunanta da ke zaune a tantuna.
Duk da kusan shekaru uku da da gwamnatin yahudawa fara tayar da zaune-tsaye a yankin, sojojin wannan gwamnati sun makale acikin wannan danbarwar yakin kuma ba su iya cimma burin da aka zayyana na yaƙin ba.
Gwamnatin yahudawa har yanzu tana cikin yaƙi a zirin Gaza da Lebanon, kuma tayar da zaune-tsaye na wannan gwamnati tare da hadin gwiwar Amurka a kan Iran shi ma ya fuskanci martani mai ƙarfi, wanda Tel Aviv da Washington sun gaza cimma burinsu na wannan tayar da zaune-tsaye.
..................
Your Comment